ABNA24 : Wata majiya daga tawagar gwamnatin Afganistan a tattaunawar Doha, da ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce gwamnatin Kaboul ta yi wa ‘yan Taliban tayin raba madafun iko da sharadin dakatar da fada.
Bukatar ta gwamnmatin Kaboul na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan kungiyar ta Taliban ke ci gaba da dannawa da nufin kwace manyan biranen kasar.
Kawo yanzu dai Taliban ta kwace ikon kashi 10 cikin 34 na manyan biranen kasar, a yayin da su ke ci gaba da kai harin kwace wasu.
Na baya bayan nan shi ne birnin Ghazni, dake nisan kilomita 150 daga kudu maso yammacin Kaboul babban birnin kasar, sai kuma wata hedikwatar ‘yan sanda a yankin Lashkar Gah.
342/