ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayyanancewa an saba yin ruwan sama a kasar Sudan tsakanin watannin Yuni da Oktoba na ko wace shekara sannan ta saba da ambaliyan ruwa irin wannan.
Kamfanin dallancin labaran gwamnatin kasar Sudan SUNA ya ce a wasu lokutan ambaliyar tana lalata kayakin da gine-ginen jama’a.a irin wannan lokuta.
A ranar alhamis da ta gabata hukumar OCHA ta majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa ambliyar ruwan ta shafi mutane 12,000 a cikin jihohi 8 daga jihohi 18 na kasar. Sannan gidaje 800 sun rushe a yayinda wasu 4,400 sun lalace.
342/