8 Agusta 2021 - 20:04
​China: An Gudanar Da Gwajin Cutar Covid- 19 Ga Mutane Miliyan 11.23 A Birnin Wuhan

Jami’an kiwon lafiya a birnin Wuhan inda cutar covir 19 ta fara bulla a shekara ta 2019 a kasar China sun killace mutane birnin sun kuma gudanar da gwaje-gwajen cutar ga mutane miliyon 11.23 cikin jimillar mutane miliyon 12 a cikin yan kwanaki.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya nakato kamganin dillancin labaran Xinhua na kasar China yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa kafin haka an sami mutane 6 dauke da cutar a yayinda wasu 12 suna dauke da alamunta.

A ranar 4 ga watan Augustan da muke ciki ne jami’an kiwon lafiya suka killace birnin sannan suka fara aikin gwajin duk mutanen birnin.

Jimillar muaten da suka kamu da cutar tun bayan bullar ta a kasar China a shekara ta 2019 93,605, sannan jimillar wadanda suka rasa rayukansu kuma sun kai 4,636.

342/