8 Agusta 2021 - 20:01
​Nasrallah: Abin Da Ya Hana Isra’ila Kai Hari Kan Labanon Shi Ne Tsoron Da Take Da Shi Na Ɓarkewar Yaƙi

Shugaban ƙungiyar Hizbullah ta ƙasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar abin da ya hana Isra’ila kawo wa Labanon hari tsawon shekaru 15 ɗin da suka gabata tun bayan yaƙin 2006, shi ne tsoron da take da shi na abin da zai biyo bayan duk wani yaƙin da zai ɓarke tsakaninta da Labanon, yana mai cewa a halin yanzu Isra’ila tana cikin damuwar ci gaba da wanzuwarta sakamakon irin ƙarfin da sansanin gwagwarmaya yayi.

ABNA24 : Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a daren jiya don tunawa da nasarar da ƙungiyar ta samu a kan Isra’ila a yaƙin da yahudawan suka ƙaddamar kan Labanon a shekara ta 2006.

Yayin da ya ke magana kan hare-haren baya-bayan nan da Isra’ila ta kawo wasu yankuna na kudancin Labanon a ranar Alhamis ɗin da ta gabata kuwa, Sayyid Nasrallah ya ce abin da ya faru a baya-bayan nan ɗin wani lamari ne mai hatsarin gaske da bai taɓa faruwa ba tsawon shekaru 15 ɗin da suka gabata, don haka ya ce wannan yana daga cikin dalilan da suka sanya dakarun Hizbullah ɗin mayar da martani cikin sauri ba tare da ɓata lokaci ba.

Shugaban ƙungiyar ta Hizbullah ya ce martanin da Hizbullah ɗin ta kai yana cikin matakin mayar da martani ga duk wani wuce gona da irin Isra’ila ne a kan Labanon, sai dai ya ja kunnen Isra’ilawan da cewa idan har suka sake kawo wa Labanon harin, to akwai yiyuwar martanin da dakarun Hizbullah ɗin za su mayar mata ba zai taƙaita kawai ga wani buɗaɗɗen waje ba ne, lamarin yana iya wucewa zuwa duk wani waje a cikin ‘Isra’ilan’.

Sayyid Nasrallah ya sake jaddada cewa ƙungiyar Hizbullah ta mallaki dubun dubatar makamai masu linzami kuma na zamani sosai waɗanda za su iya kai duk wani yanki na Isra’ilan ba tare da fuskantar wata matsala, don haka ya ja kunnen Isra’ilawan da su guji duk wani ƙoƙarin wuce gona da iri kan Labanon duk kuwa a cewarsa ba za su ji ta daɗi ba.

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ce dai jiragen yaƙin haramtacciyar ƙasar Isra’ila suka ƙaddamar da wasu hare-haren wuce gona da iri a kan wasu yankuna na Kudancin Labanon da sunan mayar da martani kan wasu rokoki da aka harba daga wajen zuwa cikin ‘Isra’ilan’ lamarin da Hizbullah ɗin ta ce ba za ta taɓa amincewa da shi ba, inda a ranar Juma’ar da ta gabata ta mayar da martani ta hanyar harba wasu makamai masu linzami zuwa wasu yankuna da suke cikin yankunan da Isra’ilan ta mamaye na ƙasar Labanon.

342/