4 Agusta 2021 - 12:11
Iran Ta Yi Gargadi Dangane Da Yunkurin Bude Wani Sabon Rikicin A Gabas Ta Tsakiya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi gargadi kana bin da ya kira yunkurin bude wani sabon babi na rikici a yankin gabas ta tsakiya ta hanyar kai wa jiragen ruwa hare-hare.

ABNA24 : A cikin bayaninsa wanda ya fitara daren jiya Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatib zadeh ya bayyana cewa, hare-haren da ake kai wa jiragen ruwa a cikin yankin tekun Fasha, hakan yana tattare da wasu boyayyun manufofi ne siyasa.

Ya ce masu yin haka su kwana da sanin cewa, Iran tana sanya ido sau da kafa a kan dukkanin take-take takensu a yankin, kuma a duk lokacin da suka nemi yin wani shishigi a kanta za su gane kurensu.

Kamar yadda kuma ya yi ishara da cewa, wadanad ba su son zaman lafiyar al’ummar yankin ne suke da hannu kai tsaye a cikin wadannan ayyuka.

A jiya Talata ne aka sanar da cewa wani katafaren jirgin ruwa da ke dauke da kayan kasuwanci wanda yake dauke da tutar kasar Singapore ya samu matsala a cikin ruwa a kusa da gabar ruwa ta Fujaira a cikin kasar hadaddiyar daular larabawa, wanda ke ake sa ran hari ne aka kai masa.

Kafin wanna lokacin ma a jiya Talata an sanar da faruwar wani lamarin makamancin hakan da wani jirgin ruwan na kasuwanci wanda yake dauke da tutar kasar Vietnam.

Har yanzu dai abbu wani cikakken bayani kan hakikanin abin da ya faru, amma hukumomin kasar hadaddiyar daular larabawa sun ce ana gudanar da bincike.

342/