ABNA24 : A wata sanarwa da ma’aikatar cikin gidan ta Nijar ta fitar da aka watsa ta gidan talabijin ɗin ƙasar a jiya Litinin ta ce an kai harin ne dai da yammacin ranar Lahadi a lokacin da maharan waɗanda ba a tantance ko su waye ba suka kai hari ƙauyen Wiye da ke gundumar Banibangou kimanin kilomita 50 daga kan iyakan ƙasar da ƙasar Mali.
Sanarwar ta ce: Maharan sun kai hari ne kan fararen hula, inda suka kashe mutane 14 ciki kuwa har da wasu ma’aikata da suke aiki a wajen.
Har ila yau sanarwar ta ci gaba da cewa har ila yau kuma mutum guda ya sami rauni wanda tuni aka kai shi birnin Yamai, babban birnin ƙasar don kula da lafiyarsa.
Sanarwar ta kammala da cewa tuni aka fara gudanar da bincike don gano waɗanda suke da hannu cikin harin don hukunta su.
Ya zuwa yanzu dai babu wani ko wata ƙungiya da ta ɗau alhakin kai harin.
Yankin na Banibangou dai yana nan tsakanin kan iyakokin ƙasashen Nijar, Burkina Faso da kuma Mali wanda shekara da shekaru kenan yake fuskantar hare-haren ƙungiyoyin ta’addanci da suke da alaƙa da ƙungiyoyin ta’addancin nan na Al-Qa’ida da kuma Daesh (ISIS).
342/