24 Yuli 2021 - 06:16
​Tsohuwar Shugabar Hukumar Kare Hakkin Bil’adana Ta MDD Zata Jagoranci Binciken Take Hakkin Bil’adama A Isara’ila

Tsohuwar shugaban hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD Navi Pillay za ta jagoranci tawagar mutane uku wadanda za su gudanar da bincike kan zarge-zagen taki hakkin bil’adama, da nuna wariyar addini da kabilanci wadanda gwamnatin haramtacciyar kasar Isara’ila ta yi a yankin Gaza na baya bayan nan.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Pillay tsohuwar alkaliya ce kuma ‘yar kasar Afirka ta kudu ce, wacce ta jagorancin hukumar ta kare hakkin bil’adama ta MDD daga shekara 2008-2014.

Labarin ya kammala da cewa binciken da tawagar za ta yi sun hada da take hakkin bil’adama a yankin zirin Gaza da kuma na yamma da gojin Jordan wanda ya hada da gabacin birnin Qudus.

342/