22 Yuli 2021 - 13:37
Iran Na Bikin Babbar Sallah A Yau Laraba

Yau Laraba, Iran ke bikin babbar Sallar.

ABNA24 : An dai takaita sallar Idin a masalatai na yankuna, a matakin yaki da annobar korona.

Baya ga Iran akwia kasashe irinsu Indiya da kuma Senegal, dake gudanar da tasu sallar a yau Laraba.

Jine dai kusan illahirin kasashen musulmi suka gudanar da sallar ta Layya.

Wannan dai shi ne karo na biyu a jere da musulmai ke gudanar da bukukuwan babbar sallah cikin yanayi na fama da annobar korona data addabi duniya, wanda ya sanya kasashe da dama suka takaita yanayin yadda aka saba gudanar sallar a shekarun baya.

342/