ABNA24 : Bayanai sun ce an samu mutum 26 da suka rasa rayukansu a yankin Kwazulu-Natal, inda nan ne aka fara samun rikicin ranar Juma’a, sai kuma wasu 19 a wajajen Johannesburg, kamar yadda alkalumman da hukumomin yankunan suka fitar.
ko a wannan Talatar, an fuskanci kone-kone da kuma wawashe dukiyoyin jama’a duk da kiraye kirayen da hukumomin kasar sukayi na a kwantar da hankali, da kuma jibge sojoji.
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana tarzomar da ta barke a yankunan biyo bayan kama Jacob Zuma a matsayin mafi muni da aka taba gani tun bayan kawo karshen mulkin wariya a kasar.
342/