17 Yuni 2021 - 13:44
​Iran Ce Kasa Ta 6 A Mallakar Fasahar Samar Da Alluran Riga Kafin Cutar Korona A Duniya

Ministan kiwon lafiya na kasar Iran ya bayyana cewa kasar Iran ta shiga cikin kasashen duniya wadanda suke da fasahar samar da alluran riga kafin cutar Korona.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya nakalto Sa’id Namaki ya na fadar haka a jiya Laraba, ya kuma kara da cewa Iran ta za ma babbar cibiyar samar da magunguna a duniya.

Banda haka ministan ya ce Iran ta na daga cikin kasashe 5 na farko a duniya, wadanda suke samar da magunguna, tun daga matakin farko har zuwa karshe.

A fagen alluran riga kafin cutar korona kuma, ministan ya ce, kasar Iran ce kasa ta 6 a duniya, wajen samarda da alluran riga kafin cutar ta korona daga matakin farko har zuwa karshe ba tare da ta neman taimkon wani daga wajen kasar ba.

Sa’id Namaki ya kammala da cewa a halin yanzu Iran ta na horar da jami’an kiwon lafiya na kasar da tsarin horaswa ta zamani wanda ake kira ‘Medical Simulators’.

342/