15 Yuni 2021 - 14:46
​Aljeriya Ta Kwace Lasicin Tashar Talabijin Ta ‘Fransa 24’ Na Aiki A Kasar

Gwamnatin kasar Aljeriya ta bada sanarwan dakatar da ofishin tashar talabijin ta France 24 mallakin gwamnatin kasar Faransa kwana guda bayan zaben majalisar dokoki a kasar.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran APS ya nakalto kakakin ma’aikatar watsa labarai na kasar Ammar belhimmer yana fadar haka a shafinsa na twitter . Ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar ta dauki wannan matakin ne don irin adawar da tashar talabijin ta France 24 ta watsa labarai take nuna kiyayya ga gwamnatin kasar da ma’aikatunta daban-daban.

Labarin ya kara da cewa gwamnatin kasar ta bawa tashar talabijin ta France 24, gargadi na karshe a ranar 13 ga watan maris da ya gabata, a kan ta daina watsa zanga-zangar mako-mako wacce ake kira Hiraku mai adawa da gwamnati wanda wasu mutanen kasar suke yi, amma tayi kunnen uwar shegu da gargadin.

Tashar ta maida martani dangane da wannan matakin da aka dauka a kanta a jiya Lahadi ba, amma daractan tashar Marc Saikali, a lokacinda ya sami takardar gargadi na watan Maris ya bayyana cewa tasharsa ta yi yin aikinta na watsa labarai ne kawai.

342/