ABNA24 : Mista Maiga ya maye gurbin Moctar Ouane, wanda sojoji suka tsare a tare da tsohon shugaban rikon kwarya na kasar Bah N’diaw a ranar 24 ga watan Mayu, kafin daga bisani su sanar da yin murabus.
Maiga ya karbi mukamin firaministan kasar ne, a dai-dai lokacin da kasar dake yammacin Afirka, ke cikin wani yanayi mai sarkakiya a dukkan fanoni.
Yanzu dai abu mafi muihimmanci dake gabansa, shi ne kokarin ganin an dage wa kasar dukkan takunkuman da kungiyoyin kasa da kasa da na shiyya suka kakabawa mata, wadanda ke zama barazana ga kasar.
Sai dai, shugaban rikon gwamnatin rikon kwayar kasar ta Mali, Assimi Goita, ya bayyana cewa, sabuwar gwamnatin za ta hanzarta yin tattaunawa da masu ruwa da tsaki, don sassauta halin da kasar ke ciki.
342/