8 Yuni 2021 - 10:42
Falasdinawa Sun Ce A Shirye Suke Su Mai Da Martani Game Da Duk Wani Makircin Isra’ila

Kungiyoyin gwagwarmaya na Falasdinawa sun bukaci Isra’ila da ta guji duk wata makarkashiya a birnin Kudus da kuma harabar Masallacin na Kudus, suna masu cewa a shirye suke su mayar da martani a kowane lokaci dangane da ayyukan mamaya da aikata laifuka na Isra’ila a yankin.

ABNA24 : A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, Hadin gwiwar kungiyoyin Falasdinawa sun ce a shirye su ke kan duk wani take-taken Isra’ila.

Ta hanyar hadin kai, fahimtar juna da kuma hanyoyi daban-daban na juriya, Falasdinawa sun sami nasarar fatattakar makiya kuma suka lalata makircinsu a birnin Kudus musamman tilastawa da kame kamen Falasdinawa, inji sanarwar.

342/