3 Yuni 2021 - 13:06
Ana Hasashen Saukar Ruwan Sama Kamar Da Bakin Kwarya A Kasar Nijar A Daminar Bana

Masu hasashen yanayi sun hango cewa daminar bana a kasar Nijar za ta zo da mamakon ruwa wanda zai iya haddasa ambaliya a wasu yankuna.

ABNA24 : Ma’aikatar gidan gona ta kasar Nijar din ta fitar da sanarwa ne akan yadda ake hasashen daminar bana za ta kasance, tun a ranar 6 ga watan Mayu 2021

Sanarwar ta kunshi cewa a daminar bana za a sami ruwan da zai dara wanda aka taba gani a kasar a tsakanin shekarar 1981 zuwa 2020, wanda zai fara daga watan Yuni zuwa Satumba 2021.

Har ila yau sanarwar ta kara da cewa; Abu ne mai yiyuwa a gabashin kasar a sami tsaikon saukar ruwan sana na kwanakin da za su haura 10. A yammacin kasar kuwa kwanakin tsaikon saukar ruwan saman ba za su wuce kwanaki 7 zuwa 10 ba.

342/