ABNA24 : Shugaba Basshar Asad ya kara da cewa; Daga cikin mutanen birnin na Doma da akwai wadanda su ka yi shahada a cikin sojojin kasar.
Shugaban na kasar Syria wanda ya ziyarci birnin Doma domin kada kuri’ar zaben shugaban kasar da ake yi, ya kara da cewa; Ziyarar da ya kai Doma, tana kara tabbatar da cewa; Babu fada a tsakanin garuruwan garin, ko mabiya wata kungiya akan wata.
Da akwai ‘yan takara biyu da suke gogayya da Basshar Asad a zaben shugaban kasar da aka bude a yau Laraba.
342/