ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya nakalto rahoto wanda farfesa Sambo Junaidu, shugaban majalisar shawara ta al-amuran addinin musulunci na Nageriya ya sanyawa hannu yana fadar haka.
Rashin samun ingantaccen rahoto kan ganin wata a daren jiya Talata ya sanya yau Laraba ta zama 30 ga watan Ramadan na wannan shekara ta 1442 A.H.
Sultan Abubakar ya taya al-ummar musulmi na Najeriya murnar salla karama, ya kuma bukacesu da su yiwa kasar nan addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali kamar yadda ya zo a cikin rahoton.
Shigowar watan Shawwwal, wata na 10 a kalandar addinin Musulunci shi ne karshen azumin na wajibi a cikin watan Ramadan ga musulmin wadanda azumi ya hau kansu.
342/