13 Mayu 2021 - 18:53
​​Zarif Ya Ki Shiga Takarar Neman Shugabancin Kasar Iran

Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya yanke shawara kan cewa ba zai shiga takarar neman kujerar shugaban kasar ba, duk tare da matsin lamba daga abokan aikinsa a cikin harkokin siyasar kasar.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Zarif ya na fadar haka a shafinsa na Instegram.

Ministan ya kara da cewa ya dauki wannan matsayan ne bayan shawara da abokan aikinsa da dama, da samun tabbacin cewa shigarsa takarar shugabancin kasar ba alkhairi ba ne ba kasar.

A jiya Talatace aka fara rijistan ‘yan saiyasa wadanda suka cika sharuddan shiga takarar shugaban kasa a zaben da za’a gudanar a cikin yan makonni masu zuwa a nan kasar Iran.

Mohammad Javad Zarif dai kwararren jami’an diblomasiyya ne wanda ya dade yana wannan aikin. Daga ciki ya taba zama jakadan kasar Iran a MDD daga 2002-2007.

342/