ABNA24 : Da yake sanar da hakan kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Sa’eed Khatibzadeh a cikin wata sanarwa, ya ce “Saboda gazawarta na magance matsalolin yankunanta, gwamnatin Morrocco, ta sake maimaita zarge-zargen karya da mara tushe kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.”
Ya kara da cewa “Abin takaici ne yadda gwamnatin Morocco, a matsayinta na shugabar kwamitin al-Quds na yanzu (na Kungiyar Hadin Kan kasashen Musulmi (OIC), ta rika goyan bayan Isra’ila da laifufukan da take aikatawa kan a masallacin Kudus.
Wannan dai martanin Iran ne ga furicin da ministan harkokin wajen kasar ta Morocco Nasser Bourita, ya yi a baya baya nan inda ya zargi Iran da cewa ta na aiwatar da ayyukan rura wutar rikici a Arewaci da Yammacin Afrika.
342/