9 Mayu 2021 - 14:06
Bam Ya Yi Ajalin Mutum Talatin A Afganistan

Fiye da mutane 30 ne suka mutu sakamakon fashewar wani bam a wajen wata makaranta a Kabul babban birnin Afghanistan.

ABNA24 : Fashewar ta faru ne a unguwar da mabiya Shi'a suka fi yawa a Dasht-e-Barchi, dake yammacin Kabul, ranar Asabar.

Kusan illahirin wadanda lamarin ya rusa dasu dalibai ne, baya ga hakan kuma akwai sama da mutum 50 da suka ji rauni.

Adadin zai iya fin hakan,”in ji kakakin ma’aikatar cikin gidan Afghanistan Tareq Arian.

Gwamnatin Afgansitan dai ta yi tir da kakkausar murya da harin, yayin da kungiyar Taliban ta musanta hannunta a harin.

A baya baya nan dai Kabul na cikin shirin ko ta kwana yayin da Amurka ta fara janye dakarunta daga kasar.

342/