ABNA24 : Dokar umarnin fadar shugaban kasa da aka fitar ta ayyana cewa, shugaban kasar ya bayar da umarnin mayar da ikon hukumomin lardunan arewa maso gabashin kasar daga hannun fararen hula zuwa hannun sojoji, inda aka sanya dokar ta baci a ‘yan kwanakin da suka gabata, da nufin dakile hare haren kungiyoyin masu dauke da makamai.
“Domin shawo kan al’amurran tsaro karkashin dokar ta bacin, shugabannin gwamnatocin fararen hula na lardunan Ituri da arewacin Kivu da wasu hukumomin lardunan za a maye gurbinsu da jami’an tsaro da na sojojin kasar ta DRC ko kuma ‘yan sandan kasar," kamar yadda kakakin shugaban kasar ya sanar.
An kafa dokar ta bacin ne tun daga ranar Alhamis inda za ta kare cikin kwanaki 30.
Da yammacin ranar Juma’a, shugaba Tshisekedi ya ayyana dokar ta bacin a lardunan kasar biyu.
A cewar kakakin gwamnatin kasar, Patrick Muyaya, shugaban kasar ya bayyana daukar wannan mataki ne tare da amincewar firaministan kasar Lukonde Sama, da kuma shugaban majalisar wakilai da na majalisar dattijan kasar.
342/