ABNA24 : Mamabobin majalisar riko kwaryar dai sun kunshi manyan jami’an soja goma sha biyar a karkashin jagoran Laftanar janar Lieutenant General Mahamat Idriss Deby.
Wannan sanarwar dai ta zo ne adaidai lokacin da jam’iyyun siyasa da kuma kungiyoyin fararen hula su ka bukaci a mika mulki ga shugaban majalisar dokoki kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanada.
A jiya ne dai aka sanar da cewa shugaban kasar ta Chadi Idriss Deby ya rasu bayan da ya sami raunkuna a filin dagar fada da ‘yan tawaye.
342/