15 Afirilu 2021 - 14:28
An Kashe Da Kuma Raunana Wasu Jami’an Кungiyar Leƙen Asirin ‘Isra’ila’ MOSSAD A Iraƙi

An hallaka da kuma raunana wasu jami’an ƙungiyar leƙen asirin Isra’ila, MOSSAD, sakamakon wani hari da aka kai wa wata cibiyar su da ke ƙasar Iraƙi, lamarin da aka bayyana shi a matsayin wani gagarumar koma baya ga ƙungiyar.

ABNA24 : Kafar watsa labaran Sabereen ta ƙasar Iraƙin ta jiyo wasu majiyoyin tsaron ƙasar suna cewa wasu mutane da ba a tantance ko su wane ne ba sun kai wani gagarumin hari kan wata cibiyar ƙungiyar MOSSAD ta ‘Isra’ilan’ da ke arewacin ƙasar Iraƙin.

Kafar watsa labaran ta ce harin da aka kai ɗin yayi sanadiyyar mutuwa da kuma raunana wani adadi na jami’an leƙen asirin ‘Isra’ilan’ da suke wajen, lamarin da ake ganinsa a matsayin gagarumar koma baya da kuma cutarwa ga ƙungiyar leƙen asirin.

Wannan lamari kuwa yana zuwa ne ‘yan sa’oi bayan wani hari da aka kai wa wani jirgin ruwan ‘Isra’ila a tashar bakin ruwan Fujairah na UAE, lamarin da aka ce ya lalata jirgin sai dai kuma babu wani da ya mutu.

Haka nan kuma dukkanin waɗannan abubuwan suna zuwa ne bayan harin zagon ƙasar da aka kai cibiyar nukiliyan Iran na Natanz da Iran ɗin ta zargi haramtacciyar ƙasar Isra’ilan da hannu cikinsa.

342/