18 Maris 2021 - 14:38
Lebanon:Hezbollah Da Rasha Sun Bukaci A Kubutar Da Dukkan Yankunan Kasar Siriya Daga Mamaya Sannan A Sake Gininta

Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbulla ta kasar Lebanon ta bayyana cewa ta cimma matsaya da gwamnatin kasar Rasha na kammala dawo da ikon gwamnatin kasar Siriya a kan dukkan yankunanta da aka mamaye sannan, sannan a sake gina ta.

ABNA24 : Ammar Al-Musawi shugaban tawagar kungiyar wacce ta ziyarci kasar Rasha a cikin yan kwanakin da suka gabata, ya fadawa tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon a jiya Talata da yamma, bayan da tawagar ta kammala ziyarar, kan cewa, akwai yiyuwan dawowar kungiyoyin yan ta’adda a kasashen Siriya da Lebanon, don haka kasar Rasha da kuma Hizbullah a shirye suke su kare kasashen daga mamaya.

Banda haka Al-Musawi ya kara da cewa batun komawar ‘yan gudun hijiran kasar Siriya wadanda suke samun mafaka a kasar Lebanon Lebanon kasarsu, na daga cikin batutuwan da suka tattauna da Jami’an gwamnatin kasar Rasha a ziyarar.

Tun shekara ta 2011 ne gwamnatin kasar Siriya take fama da kungiyoyin ‘yan ta’adda wadanda suka kwace iko da mafi yawan kasar daga hannun gwamnatin shugaba Bashar Al-Asad da farko, tare da tallafin kasashen Amurka da wasu kasashen yankin.

Amma sojojin gwamnatin kasar ta Siriya tare da tallafin kasashen Rasha da Iran da kuma kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun dawo da ikon gwamnatin kasar a mafi yawan yankunan kasar.

342/