ABNA24 : Labarin ya kara da cewa kafin haka, firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya zanta da yarima mai jiran gadon sarautar UAE Mohammad bin Za’id Aali Nahyan inda bangarorin biyu suka zanta batun huldar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.
Har’ila yau labarin ya kara da cewa kamfanonin UAE ne zasu samar da wadannan kudade wadanda za’a kashe su a bangarorin samar da makamashi, ruwa, ayyuka a sararin samaniya, kiwon lafiya da kuma fasahar noma a cikin haramtacciyar kasar.
342/