ABNA24 : A jiya ne jirgin dake dauke da kashin farko na allurarn riga kafin cutar korona na kamfanin Pfizer/BioNTech ya isa a kasar ta Labanon.
Za’a kaddamar da rigakafin ne da allurai 28,500 a wani mataki na dakile yaduwar cutar.
Firaministan kasar Hassan Diab, na daga cikin wadanda ake sa ran yiw arigakafin a wannan Lahadin.
A Labanon dai kimanin mutane sama da 330,000 aka kiyasta sun harbu da cutar ta korona a fadin kasar.
342/