ABNA24 : Babban sakatare a ma’aikatar ilimi ta tarayya ta Nijeriyan, Sonny Echono ne ya sanar da hakan, cikin wata sanarwa ga manema labarai da ya fitar a Abuja, babban birnin Tarayyar Nijeriyan inda ya ce tun daga ranar 1 ga watan Janairun da ya gabata aka fara aiwatar da wannan tsarin.
A kwanakin baya ne dai gwamnatin Tarayyar Nijeriyan bayan zaman da majalisar zartarwa ta ƙasar ta gudanar ta sanar da cewa an amince da shekaru 65 a matsayin shekarun ritaya da kuma shekaru 40 a matsayin shekarun aiki ga malamai a duk faɗin ƙasar.
Kafin hakan dai shekaru 60 shi ne shekarun ritayar malaman sannan shekarun da za a yi ana aikin shi ne shekaru 35.
Sai dai Mr. Echono ya ce wajibi ne malaman sun tabbatar da suna da cikakken lafiya kafin wannan sabon tsarin ya fara aiki a kansu yana mai cewa za a buƙaci malaman da su gudanar da gwajin lafiya tukun, wanda aka same shi da ba shi da cikakken lafiya to za a buƙaci da yayi ritaya.
342/