ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto shugaba Ramaphosa ya na fadar haka a wani jawabinda ya yi a yau Talata a taron yanar gizo na ‘tattalin arzikin duniya, inda ya kara da cewa duniya tana bukatar hadin kai don yakar cutar korona, don haka bai kamata wasu kasashe su nemi tara alluran riga kafin cutar ta korona fiye da bukatarsu ba.
Daga karshen shugaban ya ce akwai wasu kasashen da suka sayi alluran riga kafin cutar ta korona ninki hudu fiye da abinda mutanen kasashensu ke bukata.
342/