24 Janairu 2021 - 15:43
Venezuela:Shugaba Madoro Ya Ce ‘Yan Ta’adda’ Sun Kai Hari Kan wani Bututun Mai A Kasar

Shugaban kasar Venezueala Nicolas Madoro ya bada sanarwan cewa wasu wadanda ya kira ‘yan ta’adda, sun kai hari kan wani bututun iskar gas da nufin hana isar gas din zuwa wasu yankunan kasar. Larabarin ya kara da cewa harin ta’addancin ya haddasa gobara a wurin amma jami’an kwana-kwana na kamfanin man fetur na kasar PDVSA sun kuma sami nasarar kashe ta.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa shugaban ya sha zargin gwamnatocin kasashen Colombia makobciyar kasar da kuma Amurka da hannun a cikin ayyukan ta’addanci a kasarsa. Kafin haka dai Madoro ya yi maraba da tafiyar Donal Trump a matsayin shugaban kasar Amurksa, sannan ya yi kira ga sabuwar gwamnatin kasar zuwa tattaunawa da fahintar juna.

342/