ABNA24 : A tsakiyar watan Disamba da ya gabata ne, shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump, ya bayar da umarnin janye sojojin Amurka kusan 700 daga Somaliya.
Tawagar ta Africom, ta ce sojojin sun fice kwana biyu kafin wa’adin da aka dibar.
Tuni aka kaurar da dakarun zuwa wasu sansanoni, saidai tawagar ta Africom, ba ta yi karin bayyani ba kan inda aka jibge dakaraun, amma wasu sun fara tunanin ko an jibge su ne a sansanonin sojin Amurka na Kenya ko Djibouti.
Amurka ta ce kwashe dakarun na ta a Somalia, ba zai hana ta ci gaba da yakin da take da ‘yan kungiyar Al’shabab ba.
342/