31 Disamba 2020 - 13:06
Kasashen Iran, Turkiya Da Pakistan Za Su Fara Farfado Da Tsohon Layin Dogo

Kasashen Iran, Turkuya Da Pakistan Za Su Fara Farfado Da Tsohon Layin Dogo

ABNA24 : Layin dogon da kasashen Iran, Turkiya da Pakistan za su sake farfado da shi, zai kuma wuce har zuwa kasar China.

Tun a shekarar 2009 ne dai kasashen uku su ka shimfida layin jirgin kasan na jigilar kayyaki,amma har yanzu yana a matsayin na gwaji ne.

Sai dai a yanzu kasashen suna kokarin sake shimfida wani layin dogo din na jigilar matafiya da zai isa har zuwa cikin kasar Sin.

Idan aka kammala shimfida layin jirgin kasan mai cin kilo mita 6,540, zai rage dogon zangon da ake ci a ruwa na tsawon kwanaki 21 daga Pakistan zuwa Turkiya, da mayar da shi kwanaki 10 kawai.

Har ila yau layin jirgin kasan zai bunkasa harkar kasuwanci a cikin kasashen Asiya, Afirka da kuma turai.

342/