4 Disamba 2020 - 17:03
​An Tisa Keyar Abdulrashid Maina Zuwa Najeriya

Bayanai daga Najeriya na cewa an tiso keyar tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho na kasar garambawul, cewa da Abdulrashid Maina daga Jamhuriyar Nijar zuwa gida.

ABNA24 : Rahotanni sun ce ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol ne suka tiso keyar Abdulrashid Maina zuwa Najeriya, bayan an cafke shi a makobciyar kasar Jamhuriyyar Nijar a cikin wannan makon.

Ita ma dai rundinar ‘yan sanda Najeriyar ta tabbatar da lamarin a shafinta na Twitter, inda ta saka wasu hotuna dake nuna lokacin da aka maido Abdulrashid cikin wani jirgin ‘yan sandan kasar.

A ranar Litinin data gabata ne jami'an tattara bayanan sirrri a jamhuriyar Nijar suka kama Maina.

Abdulrashid Maina, na fuskantar tuhume-tuhume har guda 12 tare da wani kamfani, da hukumar yaki da yiwa tattalin arzkin kasar tu’annati ta EFCC ta gabatar.

EFCC na zargin Maina da amfani da asusun wani kamfani wajen halatta kudin haram har kusan naira biliyan biyu.

A baya dai wata babbar kotu ta ba da belinsa wanda daga bisani ya tsere, lamarin da ya sa kotun ta tsare Sanata Ali Ndume - wanda ya tsaya masa aka ba da belinsa.

Rundunar ‘yan sandan ta ce yanzu dai Abdulradhid maina zai ci gaba da fuskantar shari'a.

342/