20 Oktoba 2020 - 13:41
​Alhuthi: Larabawan Da Ke Hankoron Kulla Hulda Da Isra’ila Maciya Amana Ne

Jagoran kungiyar Ansarullah a kasar Yemen ya caccaki gwamnatocin kasashen larabawan da suke ta hankoron ganin sun kulla alaka da Isra’ila.

ABNA24 : Tashar almasirah daga birnin san’a na kasar Yemen ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani jawabi da ya gabatar a yammacin yau Litinin, Sayyid Abdulmalik Alhuthi jagoran kungiyar Ansarullah, ya bayyana cewa; wasu daga cikin sarakuna da shugabannin larabawa maciya amanar al’ummominsu, suna ta hankoron ganin sun kulla hulda da yahudawan Isra’ila, domin faranta wa iyayen gidansu da ke fadar white house a Amurka.

Ya ce wadannan sarakuna da shugabannin larabawa ba su wakiltar al’ummominsu, kamar yadda kuma ba su wakiltar al’ummomin musulmi, domin kuwa suna zartar da manufofin ‘yan mukin mallaka ne a kasashen nasu, ta hanyar yin mulkin mulukiya da kama karya, ba bisa ra’ayin jama’a ba.

Haka nan kuma ya yi ishara da yadda shugabannin Amurka da na Isra’ila suke son yin amfani da wannan batun domin cimma manufofinsu na siyasa, sakamakon bore da kakkausar suka suka daga suke fuskanta daga mutanensu.

Alhuti ya kara da cewa, dukkanin masu hankoron ganin sun burge yahudawa ta hanyar kulla alaka ko ba su damar yin amfani da sararin samaniya, irin wadannan sarakuna da shugabannin larabawa su ne suka rugurguza kasashen Syria da Yemen, tare da yin amfani da ‘yan ta’adda wajen bata sunan addinin musuluncia duniya.

342/