ABNA24 : Tashar talabijin ta Al-Alam a nan Tehran ta bayyana cewa sauke babban kwamandan sojojin kasa na kasar ta Kuwaita shi ne aiki na farko wanda sarkin ya fara yi bayan karbar ragamar shugabancin kasar. Wasu majiyoyi sun bayyana cewa mai yuwa sarkin ya fara gabatar da wadannan sauye-sauye ne don daidaita tsakanin ‘yan gidan sarautar kasar wato “Ali-Assabah”, da nufin basu wasu manya-manyan mukamai na daban na gaba. An nada Al-Khidir kan kujerar babban kwamandan sojojin kasa na kasar ne a cikin watan Octoban shekara 2014.
342/