ABNA24 : Ko da yammacin jiya Asabar ma dubban ne suka fito zanga zangar a gaban gidan Netanyahun.
Masu zanga zangar dai na sukan yadda gwamnatin Netanyahun ke tafiyar da sha’anin kiwan lafiya da yaki da annobar korona da tattalin arziki.
Wasu daga cikin masu zanga zangar kuwa na bukatar sauyi gwamnatin da suke da zargi da cin hanci da rashawa, yayin da wasu kuwa ke yin tir da yadda gwamnatin ke ci gaba da kuntatawa Falasdinawa.
A makon da ya gabata ne gwamnatin Isra’ila ta sanar da daukan sabbin matakan kulle na tsawon makwanni uku sakamakon sake dawowar annobar cutar korona, saidai wasu na ganin wannan a wani yunkurin gwamnati na hana su zanga zanga bisa fakewa da annobar ta korona.
Tun a cikin watan Yuli da ya gabata ne masu zanga zangar ke fitowa ko wanne daren Asabar domin nuna bacin ransu kan gwamnatin ta Netanyahu.
342/