23 Satumba 2020 - 10:20
Alkalin Alkalan Kenya Ya Bukaci A Rusa Majalisar Dokokin Kasar Don Mata Su Samu Wakilci

Alkalin alkalan kasar Kenya a kasar Kenya ya bukaci shugaban kasar Uhuru Kenyatta da ya rusa majalisar dokokin kasar saboda rashin cika ka’ida na samar da ‘yan majalisa mata kashi 1/3 a majalisar, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ta shekara ta 2010 ta tanadar.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto alkalin alkalan kasar mai shari’a David Maraga ya na cewa “duk tare da wanan dokar a halin yanzu mata sune rike da kashi 21% na kujeru a majalisar wakilan kasar, a yayinda suke da kashi 31% a majalisar dattawa, wanda ya nuna cewa yan majalisa maza ne suke rike da fiye da kashi 2/3 na majalisar dokokin kasar a majalisun dokokin guda biyu.

Kashi 1/3 na ma’aikatan gwamnatin miliyon 2.5 a kasar Kenya dai mata ne, sannan mata ne suke samar da kashi 80% na abincin da mutanen kasar suke ci. Amma kuma suna da, kashi 1% kacal na filayen noma a kasar.

Har’ila yau labarin ya kara da cewa wannan hukuncin shawara ce ga shugaban kasar, babu dole ciki, musamman ganin irin halin da kasar take ciki na karancin kudade.

342/