14 Satumba 2020 - 14:15
​Yedioth Ahronoth: Kulla Alaka Tsakanin Bahrain Da Isra’ila Zai Taimaka Ma Trump Da Ben Salman

Jaridar yahudawan Isra’ila ta Yedioth Ahronoth ta bayyana cewa, kulla alaka tsakanin masarautar kasar Bahrain da kuma gwamnatin Isra’ila, zai amfanar da shugaban kasar Amurka Donald Trump, da kuma Muhammad Bin Salman yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya.

ABNA24 : Jaridar ta ce, ko shakka babu kasar Bahrain ba wata kasa ce mai wani muhimmanci a yankin gabas ta tsakiya ko yankin tekun Fasha ba, amma kulla wannan alaka zai kara tabbatar da halascin Isra’ila a matsayin kasa, wadda hatta kasashen larabawa sun amince da ita.

Jaridar ta ce tun a cikin shekarun 1990 akwai alaka mai karfi tsakanin wadannan kasashe da kuma Isra’ila, musamman UAE, amma fitowa fili a sanar da wannan alaka a hukuamnce babban lamari ne mai matukar muhimmanci ga Isra’ila.

Haka nan kuma jaridar ta yi ishara da cewa, kasar Bahrain mafi yawan mutanen kasarta mabiya mazhabar shi’a ne, sabanin kasashen UAE da Oman.

Baya ga haka kuma jaridar ta ce wannan lamari ya faru ne bayan cimma matsaya tsakanin Trump da kuma Muhammad Ben Salman, wanda hakan zai kara daga matsayin Ben Salman a matsayin mai karfin fada a ji a yankin, kamar yadda shi kuma Trump hakan zai taimaka masa a yakin neman zabe, wata kila ma har ya samu kyautar nobel ta zaman lafiya.

342/