ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran SANA na gwamnatin kasar ta Syriya ya nakalto Elexander Grankovich wani babban jami’a a ma’aikatan tsaron kasar ta Rasha yana fadar haka.
Ya kuma kara da cewa “rahotannin sirri da muka samu sun nuna cewa kungiyar ta gayyaci yan jiridu daga kasashen waje zuwa Jabal Zawiya don daukar daukar hotunan hare haren na guba kan mutanen lardin idlib sannan su yi amfani da su don zargin sojojin gwamnatin kasar Syriya da aikta laifin.
Gwamnatin kasar Amurka da kawayenta a yankin kudancin Asia suna tsoron faduwar kungiyoyin ‘yan ta’adda wadanda suka kirkiro a kasar ta Syriya.
342/