ABNA24 : Yankunan da za a sake saben a cikinsu sun kunshi gundumomi 8 za kuma a dauki sa’oi 10 ana kada kuri’a.
Da akwai ‘yan takara 20 da suke gogayya da juna domin samun kujerun 10 na majalisar shawarar musulunci ta Iran.
Kakakin majalisar kare tsarin mulki wacce take kula da zaben Abbas Kad, Khudai ya sanar da aike tawaga 24 domin sa ido a yadda ake gudanar da zaben a dukkanin wurare 20 da ake yin zaben.
Bugu da kari ana yin zaben ne a cikin kula da dukkanin matakan kiwon lafiya na fada da cutar corona.
342/