ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto ministan ya na fadar haka a jiya Lahadi a lokacinda yake magana dangane da kissan sojojin kasar guda biyu a kasar Mali a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.
Kafin haka dai fadar Elize ta bada sanarwan mutuwar sojojin kasar Faransa biyu a kasar Mali a jiya Lahadi.
Har’ila yau ministan tsaron na kasar ta Farasna ya bukaci gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ta matsawa sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Mali lamba, don su gaggauta maida mulki ga fararen-hula a kasar.
Tun shekara ta 2013 ne gwamnatin kasar Faransa ta shigo da sojojinta kasar ta Mali da sunan yaki da ‘yan ta’adda wadanda suke mamaye da arewacin kasar a lokacin.
342/