ABNA24 : Mista Akinwunmi, zai jagoranci bankin na karin wasu shekara biyar a wa’adi na biyu.
Tsohon ministan aikin gona na Najeriya ya dai lashe zaben ne babu abokin hammaya.
A kwanakin baya ne wani kwamiti na musamman da aka kafa ya wanke Adesina, daga zargin nuna bambamci tare da fifita ‘yan Najeriya wajen bayar da aiki da kuma kwangiloli a bankin na AfDB.
A jawabinsa na soma aiki a karo na biyu, Mista Adesina ya ce zai mayar da hankali kan yin aiki tukuru domin ci gaban nahiyar Afrika ba tare da nuna son zuciya ba.
342/