ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Jean-Yves Le Drian yana fadar haka a safiyar yau a ma’aikatar tsaron kasar da ke birnin Prais.Jean-Yves Le Drian ya kara da cewa juyin mulkin ba zai hana sojojin kasar Faransa ci gaba da ayyukansu na yaki da ‘yan ta’adda a kasar ba.Sai dai a tattaunawa tsakanin tawagar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ECOWAS a ranar 18 ga watan Augustan da muke ciki, sojojin sun ce gwamnatin rikon kwarya a kasar zata dauki shekaru 3 cur kafin su mika mulki ga fararen hula.Kasar Faransa dai tana da sojoji 5100 a yankin Sahel mafi yawansu suna kasar Mali ne.
342/