24 Agusta 2020 - 14:50
Yemen : Makiya Za Su Yaba Wa Aya-zaki

Ministan tsaron kasar ta Yemen janar Muhammad Nasir al-Atify ya bayyana cewa; Kwanaki da watanni masu zuwa suna cike da abubuwan mamaki da makiya za su gani, kuma su yabawa aya zaki.

ABNA24 : Ministan tsaron kasar ta yemen wanda ya ke ganawa da sojojin kasar da kuma dakarun sa-kai na al’umma ya kara da cewa; Makiya sun kasa cimma manufofinsu na soja, siyasa da tattalin arziki saboda tsayin daka da kuma juriyar al’ummar Yemen da jarurcewarsu a fagen yaki.

A nasu gefen, sojoji da mayakan na kasar Yemen sun jaddada alkawalin ci gaba da sauke nauyin da ke wuyansu na yaki da makiya da kare kasa da sadaukar da kawukansu.

Kasar ta Yemen dai tana fuskantar yakin wuce gona da iri daga Saudiyya da kawancen da ta kafa tun a daga shekarar 2015.

Dubun dubatar mutanen kasar ta Yemen ne dai su ka kwanta dama saboda hare-haren na Saudiyya da kawayenta,yayin da wasu adadi masu yawa su ka jikkata.

Har ila yau hare-haren na Saudiyya sun lalata asibitoci da cibiyoyin shan magani a cikin kasar Yemen da hakan ya mayar da yaki da cutar corona zama abu mai wuya.

342/