18 Agusta 2020 - 10:34
AfCFTA Na Sa Ran Cimma Yarjejeniyar Cinikayya Ta Farko A 2021

Tarayyar Afrika ta sanar da cewa, ana sa ran cimma yarjejeniyar cinikayya marar shinge ta nahiyar, a ranar 1 ga watan Junairun 2021, yayin da za a ci gaba da tattaunawa ta kafar intanet.

ABNA24 : Sakatare Janar na yankin, Wamkele Mene, ya bayyana cikin watan Afrilu cewa, kaddamar da yarjejeniyar ba zai gudana a ranar 1 ga watan Yuli ba kamar yadda aka tsara, saboda annobar COVID-19.

A cewar AU, yarjejeniyar za ta bai wa nahiyar damar daidaita sarin samar da kayayyaki, da rage dogaro kan wasu da kuma gaggauta kafa hanyoyin samar da kayayyaki a yankuna, wanda zai bunkasa cinikayya tsakanin kasashen nahiyar.

Wani rahoton bankin duniya ya bayyana cewa, nasarar kaddamar da yarjejeniyar za ta magance tasirin COVID-19 kan ci gaban tattalin arziki ta hanyar bunkasa cinikayya tsakanin yankuna da rage tsadar cinikayyar.

Ya kara da cewa, galibin kudin shigar yankin zai samu ne idan ya fara aiki, kana aka saukaka tsarukan kwastam.

342/