ABNA24 : Da yake sanar da hakan ministan lafiya na kasar Rashar, Mikhail Murashko, ya ce bisa ga dukkan alamu takwarorinmu sun fara nuna damuwa kan maganin da muka samar, saidai damuwar tasu ba tada hujja.
Ministan lafiyar na Rasha ya ce nan da makwanni biyu za’a fitar kashin farko na rigakafin wanda kuma za’a fara yi wa ma’aikatan lafiya.
Wannan dai na zuwa ne bayan da kasashen Jamus, Faransa, Espain, da kuma Amurka suka bukaci a yi taka tsan-tsan kan rigakafin da Rashar ta sanar ta samu na cutar ta Korona.
A ranar talatar data gabata ce shugaban kasar Rashar, Vladimir Poutine, ya sanar da cewa kasarsa ta samo rigakafin cutar korona na farko a duniya.
Kuma ya ce maganin ‘’Sputnik V’’ yana da tabas da kuma inganci, don kuwa hatta ‘yarsa guda an gwada maganin a kanta.
Tuni dai hukumar lafiya ta duniya, ta sanar cewa ta fara tattaunawa da kasar Rashar game da riga kafin.
342/