ABNA24 : Da yake tabbatar da hakan gwamnan jihar Tillabery, Tidjani Ibrahim Katiella, ya ce mutanen da aka kashe sun hada da ‘yan Nijar biyu, dreba da kuma mai rakiyar ‘yan yawan bude ido, da kuma faransawa ‘yan yawan bude ido guda shida.
Hukumomin yankin sun ce nan gaba zasuyi karin bayyani dalla-dalla kan yadda lamarin, ya auku, dama wadanda ke da alhakin kai harin.
Wasu bayyanai na daban sun ce labarin ya faru ne wajajen karfe 11H30 (10H30 GMT) a gabashin yankin ‘’Kouré" dake nisan tafiya ta awa daga Yamai babban birnin kasar.
Wata majiya a ma’aikatar gandun daji ta kasar ta ce dukkan mutanen sun mutu ne sanadin harbin bindiga, sai wata mata guda data gudu amma ita a daga bisani an kashe ta hanyar yi mata yankan rago.
Wannan dai shi ne hari irinsa na farko kan ‘yan yawan bude na kasashen yamma a wannan yankin, tun bayan da yankin yay i kaurin suna wajen samun ziyartar ‘yan yawan bude ido shekaru 20 da suka gabata saboda rakumman daji da ya kunsa.
Yankin Tillabery dai ya jima yana fuskntar hare hara na mayakan dake ikirari da sunan jihadi musamman a iyakokin da suka hada Nijar, Burkina Faso da kuma Mali, wannan ne ya sanya hukumomin kasar ayyana dokar hana zurga zurga Babura a yankin ba dare ba rana.
342/