5 Agusta 2020 - 12:39
Iran Ta Jajantawa Lebanon Game Da Fashewar Data Auku

Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta aike da sakon jaje da ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar kasar Lebanon, biyo bayan ifti’la’in fashewar data auku.

ABNA: Shugaban kasar Hassan Rohani, ya ce Iran a shirye ta ke ta bada tallafin da kasar ta Lebanoin ke bukata.

Dama kafin hakan Iran, ta bakin ministan harkokin wajenta, Mohammad Javad Zarif, ta ce tana tare da al’ummar Lebanon, a wannan lokaci na bakin ciki, kuma a shirye ta ke ta taimaka a duk inda kasar ke bukatar taimako.

Ko baya ga Iran, kasashen duniya da dama na turai da Amurka, da gabas ta tsakiya da Afrika da kuma MDD sun aike da irin wannan sakon suna masu cewa a shirye su ke su taimakawa kasar ta Lebanon da tallafi biyo bayan wannan iftila’in da ya auka mata a jiya.

342/