2 Agusta 2020 - 11:06
Sehun Borno Na Najeriya Ya Yi Koken Rashin Tsaro Da Jahar Take Fama Da Shi

Shehun Borno Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi wanda ya kai ziyarar ban girma da gaisuwar salla ga gwamnan jahar Babagana Umara Zulum kwanaki kadan bayan harin da aka kai masa, ya bayyana cewa; A halin yanzu ba mu da tsaro ko kadan.”

ABNA: A ranar Larabar da ta gabata ne dai aka kai wa tawagar gwamnan na jahar Borno hari a barin Baga da ke karamar hukumar Kukawa a wata ziyara da ya kai.”

Shehun Borno ya ci gaba da cewa; Mai girma gwamna, ko kadan ba mu ji dadi ba akan abinda ya faru a Baga,abu ne maras dadi da ban takaici.”

Shehun Borno ya kara da cewa; Idan har za a kai hari akan tawagar babban jami’in tsaro na jaha, to wallahi babu wani daga cikinmu wanda yake da tsaro ko kadan.”

Kasa da sa’o’i 24 daga kai wa tawagar gwamnan hari, an kai wasu hare-hare da makaman roka-roka a cikin birnin Maiduguri wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 4 da jikkata wasu da dama.

342/