21 Yuli 2020 - 12:53
Ivory Coast:Jam’iyyar Shugaba Watara Ta Bukace Shi Ya Shiga Takarar Shugaban Kasa Mai Zuwa

Jam’iyya mai mulkin kasar Ivory Coast ta bada sanarwan cewa ta gabatar da bukata ga shugaban kasa mai ci Alasan Watara na ya tsayawa jam’iyyar takarar shugaban kasa karo na uku a zaben karshen wannan shekara.

ABNA24: Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto shugaban jam’iyyar ta RHDP Adama Bictogo yana fadar haka a yau Litinin bayan sun fadawa shugaban wannan bukatar a yau litinin.

Adama ya kara da cewa a halin yanzu bamu da wani zabi in banda shi, sai dai idan har yak i amincewa.

Kafin haka dai shugaban ya bayyana cewa ba zai tsayawa jam’iyyar takarar shugaban kasa a zabe nag aba ba, maimakon haka ya zabi firai ministan Amadou Gon Coulibaly, a matsayin wanda zai tsayawa jam’iyyar takara, amma sai Amadou Gon Coulibaly, ya rasu a ranar 8 ga wannan watan da muke ciki sanadiyyar cutar zuciya.

Adama ya bayyana cewa shugaban zai basu amsa nan da ‘yan kwanaki don su san abinda zasu yi. PDCI

Ana saran Henri Konan Bedie dan takar jam’iyyar adawa mafi girma a kasar, wato PDCI zai shiga takarar shugaban kasa a zaben na ranar 30 ga watan Octoba. Mai yuwa ya kara da shugaban watara idan har ya amince da bukatar jam’iyyarsa.

342/