21 Yuli 2020 - 12:44
Shugabannin Afrika Za Su Isa Mali, Domin Sasanta Rikicin Kasar

Shugabannin kasashen Afrika 5 na kan hanyarsu ta zuwa Bamako na kasar Mali domin shiga tattaunawar sulhu da ake ci gaba da yi a kasar.

ABNA24: Shugabannin 5 sun hada da na Ivory Coast da Ghana da Senegal da Nijar, wadanda ake sa ran su shiga tattaunawar a Bamako a ranar Alhamis.

Har yanzu dai tsugunne bata kare ba a kasar ta Mali, inda bangarorin dake bore a kasar ke bukatar Shugaba Ibrahim Boubakar Keita ya yi murabus bisa zarginsa da gazawa saboda rashin tsaro da matsalar cin hanci da matsalar tattalin arzikin kasar.

Kafin hakan dai tawagar kungiyar Ecowas, wacce ta kammala ziyararta a Mali, ta gaza warware rikicin kasar, inda shirin da ta gabatar na warware rikicin siyasar kasar bai samu karbuwa ba wajen ‘yan adawan kasar.

Daga cikin washarwarin da tawagar ta Ecowas ta gabatar da akwai shawawar ganin na kafa gwamnatin hadin kan kasa wacce ta kunshi kashi 50 cikin dari na mambobin masu mulki.

Haka kuma kungiyar ta Ecowas ta bukaci a girka mambobin kotun tsarin mulkin kasar domin su tattauna batun sabanin dake akwai kan sakamakon zaben ‘yan majalisar dokokin kasar na baya bayan nan.

Kwamitin kungiyar ta Ecowas, na mai bukatar kuma gudanar da bincike domin zakulo wadanda bude wuta kan masu zanga zanga da kuma wadanda suka lalata wasu cibiyoyin gwamnati.

Kuma kungiyar ta Ecowas na mai fatan a cimma wadanda batutuwa kafin nan da ranar 31 ga watan Yuli, domin kasar ta Mali ta samu sukunin zama lafiya.

342/