19 Yuli 2020 - 13:49
​Zarif ya Fara Gudanar Da Ziyarar Aiki A Kasar Iraki

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya fara gudanar da ziyarar aiki a yau Lahadi a kasar Iraki.

ABNA24: Kamfanin dillancin labaran Iran kasar Iran IRNA ya bayar da rahoton cewa, a yau ministan harkokin wajen kasar Muhammad Jawad Zarif ya isa birnin Bagadaza domin gudanar da ziyarar aiki a kasar Iraki.

Bayan isarsa birnin Bagadaza, Zarif ya fara da ziyaratar wurin da aka kashe Janar Kasim Sulaimani, a kusa da babban filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Bagadaza.

A yayin ziyarar tasa, zarif zai gana da takwaransa na Iraki Fu’ad Hussain, daga nan kuma zai gana shugaban kasar ta Iraki Barham Saleh, da kuma Firayi ministan kasar Mustafa Kazimi, sai kuma shugaban majalisar dokokin kasar Muhammad Al-halbusi, da kuma shugaban rundunar dakarun sa kai ta Hash Al-sha’abi Falih Fayyad.

Babbar manufar ziyarar dai ita ce kara karfafa alaka tsakanin kasashen Iran da Iraki a dukkanin bangarori.

342/